Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Damfara Sun Shiga Hannu A Jhar Oyo


'ya'yan itace a kasuwa
'ya'yan itace a kasuwa

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Oyo ta damke wadansu mutane da suka zambaci mata kimanin dari uku miliyoyin Nairori, inda suka bude ofishin a birnin Ibadan suka nemi matan ‘yan kasuwa su rika zuba kudi naira dubu hudu da dari biyar ko fi kowacce rana.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Oyo ta damke wadansu mutane da suka zambaci mata kimanin dari uku miliyoyin Nairori. Mazambatan sun bude ofishin a birnin Ibadan inda suka nemi matan ‘yan kasuwa da su rika zuba kudi naira dubu hudu da dari biyar ko fi kowacce ranar Allah ta allah.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Oyo Mr Kunle Ajesibutu ya bayyanawa wani taron manema labarai cewa, an kama mutane goma sha daya daga cikin wandanda suka damfari matan, suna kuma ci gaba da neman ainihin madugun damfarar da suke kyautata zaton za a kama ba da dadewa ba.

Daya daga cikin matan da aka zambata ta shaidawa wakilinmu Hasssan Umaru Tambuwal cewa, ‘yan damfarar sun aika masu da sakon kar ta kwana cewa, akwai wani taro da karfe biyu na yamma, amma da karfe goma sha biyu na rana ta fahimci cewa, mutanen ‘yan damfara ne, bayanda suka je harabar ofishin ‘yan damfarar kuma sai masu gidan suka koresu, sai dai tace, kamata ya yi kafin mai gida ya bada haya ya tantance irin mutanen da yake hulda da su.

Wannan dai ba shine karo na farko da ake irin wannan yaudarar ba. Shekaru takwas da suka shige, wadansu mutane suka bullo da wani banki da suke kira “Wonder Bank” a jihar Oyo inda suka yiwa mutane da dama awon gaba da miliyoyin nairori.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Hassan Umaru Tambuwal ya aiko.

‘Yan Damfara Sun Shiga Hannu A Jhar Oyo - 2'10"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG