A yau Alhamis ake sa ran, kwamitin da ke kula da fannin shari’a a Majalisar Wakilan Amurka, zai amince da wasu tuhume-tuhume guda biyu na tsige Shugaban kasar, Donald Trump.
Wannan wani yunkuri ne da majalisar wakilan mai rinjayen ‘yan Democrat ke yi, na tabbatar da ganin an hukunta shugaban kan laifukan da suka ce ya tafka ta hanyar amfani da mukaminsa.
'Yan Republican dai na adawa da daukacin lamarin, abin da suke kwatantawa a matsayin bi-ta-da-kullin-siyasa.
“Wannan ba a abin da ya kai a tsige shugaban kasa ba ne, bayan shekaru da aka kwashe ana bincike mara kan-gado.” A cewar dan majalisar wakilai Matt Gaezt, na jam’iyyar Republican.
Kwamitin ya kwashe daren jiya Laraba, yana muhawara kan tuhume-tuhumen, wadanda suke nuni da cewa Shugaba Trump ya wuce gona da iri, da ya tursasa gwamnatin wata kasar waje - wato Ukraine, ta sa hannu a zaben Amurka na 2020, ta hanyar binciken abokanan hamayyarsa na siyasa.
Daya tuhumar, ta shafi umurnin da Shugaba Trump ya bai wa jami’an gwamnatinsa ne, na kada su bayyana a gaban majalisar wakilan da ke binciken lamarin.
Za ku iya son wannan ma
-
Mayu 25, 2023
Tina Turner, ta rasu tana da shekara 83
-
Mayu 18, 2023
Dan Najeriya Ya Zama Magajin Garin Colorado Springs
-
Mayu 15, 2023
Amurka Za Ta Hana Biza Ga Wasu 'Yan Najeriya
Facebook Forum