'Yan fanshon na wannan taron ne a kokarinsu na musanta zancen bangaren gwamnatin jihar, da take cewa ta biya dukkan kudaden fansho da garatuti ga ma’aikatan da suka bar aiki, ciki ko har da wadanda ta tarar suna bin bashi.
Babangida Garba Gwandu, shine shugaban ‘yan fanshon masu bin kadin hakkin su a jihar ta Kebbi. Yace maganganun da wasu shugabannin jihar suka yi babu gaskiya a ciki. Ya kuma tabbatar da cewa ba a biya jama’a da yawa kudadensu ba.
Bala Sani birnin Kebbi, na daya daga cikin ‘yan fanshon da suka tattaru a filin idin, yace ya kamata a ce an biya su hakkinsu duk da cewa sun bi duk hanyoyin da suka dace amma har yanzu hakar su bata cimma ruwa ba. Ya kuma ce cikin matsalolin da suke fuskanta har da rashin abinci, kuma an koro ‘yayansu daga makaranta.
Shi kuma kakakin jam’iyyar APC na jihar Kebbi, kuma shugaban kwamitin yakin neman zabe Alhaji Sani Dododo, an ruwaito yana fadin cewa gwamnatin jihar ta biya dukkan hakkokin ‘yan fanshon.
Ga karin bayani cikin sauti daga Murtla Faruk Sanyinna.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 29, 2023
CBN Ya Kara Kwana 10 Kan Wa’adin Daina Karbar Tsofaffin Kudi
-
Janairu 27, 2023
Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Kauce Hanya
-
Janairu 27, 2023
Za Mu Daukaka Kara – Adeleke
Facebook Forum