Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Firamare a Jihar Adamawa Sun Yi Addu'o'i da Kuka Akan Ta'dancin Boko Haram


Yara
Yara

A jihar Adamawa yara 'yan firamare da shugabannin addinai suka tara sun yi addu'o'i da kuka wa Ubangiji domin ya kawar da masifar da 'yan Boko Haram suka jefa jihar ciki da wasu wuraren a Najeriya.

Daliban makarantun firamare kusan dubu biyu suka hallara wirin addu'o'in inda suka nuna bakin cikinsu da juyayi sabili da aika-aikar 'yan kungiyar Boko Haram a jiharsu.

Kawo yanzu 'yan Boko Haram suna rike da kananan hukumomin jihar guda hudu kuma suna cigaba da fadadawa tare da kame wasu yankunan.

Rabaran Dauda Clifford wakilin kungiyar kiristocin Najeriya a wurin addu'o'in yace sun bada gaskiya cewa idan an hada yin addu'a da yara suka yi kuka Ubangiji zai ji tausayi ya ceci al'ummarsa. Zai ji tausayi ya raba kasar daga masifar Boko Haram da ta shiga. Yace lokacin yakin basasa na Biafra yara sun dukufa da addu'o'i domin kada kasar ta rabu kuma Ubangiji yaci.

Alhaji Abdullahi Damari na kungiyar dake shiga tsakanin musulmai da kiristoci yana cikin waddanda suka shirya taron. Malamai sun ce Allah na karbar addu'ar yara da wuri. Haka kuma yana karbar addu'ar marayu da waddanda aka zalunta.

To amma 'yan Boko Haram na cigaba da kafa daularsu. Yanzu ma sun fada yankin Maiha inda suka fatattaki sojojin dake garin. Sun kashe sojoji da dama a wurin kana sauran sun gudu.

A wata sabuwa kuma rundunar 'yansandan jihar ta Adamawa ba bada sanarwar sace Alhaji Sani Ribadu kanin tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu. Wai wasu mutane uku suka je gonarsa suka saceshi.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG