Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Guatemala Sun Kira Shugaban Kasar Ya Yi Murabus A Kan Sabon Kasafin Kudi


Masu zanga zanga a Guatemala
Masu zanga zanga a Guatemala

A jiya Asabar daruruwan masu zanga zanga a Guatemala sun abka cikin wani bangaren ginin majalisar dokoki kasar yayin da ake kara kaimin zanga zangar kin jinin matakin shugaba Aljendro Giammattei da na majalisar a kan tabbatar da kasafin kudi da ya rage kason ilimi da na kiwon lafiya.

Zanga zangar ta barke ne a lokacin da kimanin mutum dubu bakwai suka yi tattaki zuwa fadar kasa a babban birnin Guatemala domin nuna rashin amincewa da kasafin kudin, da masu zanga zangar suka ce an tattauna kana aka tabbatar da shi a cikin sirri, a lokacin da kasar ta Amurka ta Tsakiya take fama da barnar mahaukatan guguwa guda biyu lokaci guda da ta COVID-19.

Wasu hotunan bidiyo da aka kafe a shafukan sada zumunta sun nuna wuta na fita ta tagar ginin majalisar. Rahotanni kafafen labarai sun ce jami’an tsaro sun harba barkonon tsohuwa kana mutane sun jikata.

Shugaba Giammatei ya yi Allah wadai da tada wutar a wani sakonsa na twitter a jiya Asabar.

Ya ce “Duk wanda aka same shi da aikata ba daidai ba za a hukunta shi ta hanyar amfani da dokokin kasa.” Ya rubuta cewa yana kare hakkin mutane su gudanar da zanga zanga, amma kuma ya ce ba zamu lamunta da lalata kadarorin jama’a da na daidaikun mutane.”

Shugaban kasar yana ganawa da kungiyoyi daban daban domin gudanar da sauye sauye a kasafin kudin mai tsarkakiya.

Mataimakin shugaban kasa Guillermo Castillo ya bayyana aniyarsa na yin murabus, ya kuma shawarci shugaba Giammatei dukkanin da su ajiye aiki tare saboda zaman lafiyar kasar.

Giammatei bai maida martani a kan shawarar a bainin jama’a ba tukuna, kana shima Castillo bai bayyana martanin shugaban game da shawarar da ya shi. Castillo ya ce ba zai yi murabus shi kadai ba.

An shirya tsarin kashe kudin ne a cikin sirri kana majalisar dokokin ta tabbatar da kudurin da sanyin safiyar ranar Laraba. Tabbatar da kasafin kudin ya biyo bayan barna da mutuwar da mahaukatan guguwar Eta da Iota suka haddasa, wanda ya haifar da ruwan sama kamar da bakin kwarya a nahiyar Amurka ta Tsakiya.

Shugabannin mujami’ar Katolika a Guatemala kuma sun yi kira ga shugaba Giammatei a ranar da ya janye kasasfin kudin.

XS
SM
MD
LG