Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijira 23,000 Suka Tsere Daga Najeriya Zuwa Nijer a Wata Guda


Rikici da tashe-tashen hankula a Najeriya ya tilastawa 'yan gudun hijira 23,000 tserewa zuwa Jamhuriyyar Nijer a cikin wata guda.

A cikin wani takaitaccen bayanin da kakakin hukumar ‘yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya wato UNHCR Babar Baloch ya fada a taron manema labarai a yau a Palais des Nations a Geneva, ya ce, rikicin da ke ci gaba da faruwa a wasu sassan yankin Arewa maso-gabashin Najeriya ya tilastawa mutane kimanin 23,000 arcewa a cikin watan Afrilu kadai.

"Tun daga watan Afrilun shekarar 2019, mutane suke arcewa daga munanan hare-hare ta kungiyoyin ‘yan bindiga daga jihohin Sakkwato, Zamfara da Katsina na Najeriya, zuwa yankin Maradi na jamhuriyyar Nijar".

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR, ta damu matuka game da tabarbarewar tsaro a cikin Najeriya da kuma hadarin kai hare-hare a cikin jamhuriyar Nijar.

'Yan bindiga sun kai hare-hare a kauyuka da dama. Harin mafi muni da ya yi sanadiyar rayuka 47 a kananan hukumomin Kankara, Danmusa da Dusi-ma a cikin jihar Katsina.

Gwamnatin Nijer na bawa 'Yan gudun hijirar daga Najeriya izinin shiga kasar tare da basu kariya, duk da cewa an rufe kan iyakokin kasar saboda yaduwar annobar COVID-19. Sabbin kwararar ‘yan gudun hijirar akasarinsu mata da kananan yara, suna cikin tsananin bukatar ruwa, abinci da kuma kiwon lafiya, har ma da matsuguni da sutura.

Kusan kashi 95% na 'yan gudun hijirar sun fito ne daga jihar Sakkwato ta Najeriya, ragowar sun fito daga jihohin Kano, Zamfara da Katsina, inda ake hasashen samun tashe-tashen hankula masu alaka da rikicin tsakanin manoma da makiyaya. .

Babar Baloch ya ce, “mu na aiki kafada da kafada da hukumomi a Jamhuriyar Nijar domin mayar da ‘yan gudun hijirar akalla 7,000 zuwa wurin da za'a iya samar musu da ruwa, abinci, mafaka, kula da lafiyarsu da sauran muhimman bukatu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG