Accessibility links

'Yan Gudun Hijira daga Borno da Yaron da Aka Yanka Mahaifinsa Sun Isa Gombe


Sadiq, yaron da 'yanbindiga suka yanka mahaifinsa a gabansa a jihar Borno

'Yan gudun hijira daga jihar Borno fiye da dubu goma sun kwarara zuwa jihar Gombe domin neman mafaka.

Wasu 'yan gudun hijira da tashin hankalin jihar Borno ya shafa sun isa jihar Gombe domin neman tsira da ransu.

Wakilin Muryar Amurka ya samu ya zanta da wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da yanzu suna jihar Gombe. Wata Jummai Gambo tace sun taso ne game da tashin hankalin Borno. Ranar Asabar suka isa Gombe. Ita da yaranta su goma sha uku ne. Inji Jummai motar Dangote suka shigo aka saukesu a Potiskum daga can kuma wani bawan Allah ya taimakesu. A garin Gombe wani Musa Kwari ya karbesu kuma shi ne yake ciyar dasu.

Yawancin 'yan gudun hijiran mata ne da yara kanana domin ko an kashe mazan ko kuma wasu sun samu sun tsere ba'a san inda suke ba. Zainab Gambo tace su kam Maiduguri ya gagaresu bisa ga abubuwan dake faruwa. Tace a Gombe hankalinsu ya kwanta.

A wani gidan inda 'yan gudun hijirar suke wakilinmu ya ga wasu har da wani yaro dan shekara bakwai a cikinsu. Yaron mai suna Sadiq yace 'yanbindiga sun yanka mahaifinsa yayin da mahaifiyarsa ta gudu da kaninsa.

Hajiya Laraba Ahmed Kawu daraktan hukumar samarda agajin gaggawa ta jihar Gombe ta kara haske kan 'yan gudun hijiran da yadda yaron ya fada hannunta wanda take kulawa da shi a gidanta. Tace a cikin garin Gombe 'yan gudun hijiran sun fi dubu goma. Dangane da yaron Sadiq tace wata jami'a ce daga karamar hukumar Gombe ta buga mata waya tace wasu direbobi sun tsinci yaro yana gudu a daji sai suka dauko shi suka mikawa jami'an dake kula da rayuwar jama'a. Tace sun dauki duk wani bayani daga yaron sun tura Maiduguri. Yanzu suna jiran su ji abun da za'a yi nan gaba. Idan an gano mahaifiyarsa da 'yanuwansa zasu mayarda shi wurinsu.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.

XS
SM
MD
LG