Accessibility links

Yawan Hare-hare a Jihar Borno na Son Kawo Cikkas ga Harkokin Rayuwa


'Yan gudun hijira a jihar Borno

Al'ummar jihar Borno sun shiga wani hali na mawuyacin rayuwa sibili da yawan hare-hare da 'yan tsagera ke kaiwa ba dare ba rana a koina har ma da wuraren ibada.

Rayuwa a jihar Borno na son daukan wani salo inda kullum 'yanbindiga sai kashe mutane su keyi a kauyuka da birane har ma wuraren ibada basu tsira ba.

Yanzu dai harkokin kasuwanci da alamuran yau da kullum na neman tsayawa cik a kauyuka da manyan garuruwa har ma da babban birnin jihar wato Maiduguri. Hakan na faruwa ne sabili da hare haren da 'yanbindiga ke yawan kaiwa. Kusan duk wayewar gari sai an samu matsalar hare-hare a kauyuka ko garuruwa dake hallaka mutane da dama da asarar dimbin dukiyoyi.

Maharan sukan kai hari ne kan jami'an tsaro da fararen hula da yara da mata musamman 'yan makaranta. Idan sun kai hari sukan dauki lokaci mai tsawo su yi yadda suke so ba tare da jami'an tsaro sun tunkaresu ba ko kuma ba tare da wata fargaba ba. Lamarin ya sa yawancin mutanen dake zaune a kauyuka sun kaura zuwa wasu garuruwa domin tira da ransu.

Ko a daren Asabar da misalin karfe bakwai sai da aka kai hari a wani kauye inda aka hallaka mutane 47 da kona masu gidajensu da dukiyoyinsu . Wasu kuma 20 sun jikata yawancinsu mata da yara. Wasu kuma daga garin Mafa sun tasllake rijiya da baya yayin da suka arce zuwa birnin Maiduguri bayan wani mugun hari da aka kai garin misalin karfe bakwai na yamma ranar Lahadi. A garin an hallaka wasu mutane 32. Su ma an kona masu dukiya kuma tamkar ilahirin garin an koneshi.

Wasu da suka fito daga Mafa sun ce misalin karfe bakwai da rabi sai suka ji an fara harba bindiga. Wadanda suna cikin masallaci suna salla 'yanbindigan sun rufe masallacin kana suka jefa masu bam wanda ya hallakasu duka. Bayan hakan sun kone motoci da dukiyoyi. Wani yace cikin iyalansa 15 hudu kawai ya samu sauran sun tsere daji. Har makarantu maharan basu bari ba. Sun kone gidajen 'yansanda da ofishinsu.

Ga rahoto.

XS
SM
MD
LG