Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijira Daga Darfur Sun Fara Komawa Gida.


Wata 'yarinya karama take dauraya a sansanin 'yan gudun hijira daga Darfur, dake sansanin Iridimi a Cadi.
Wata 'yarinya karama take dauraya a sansanin 'yan gudun hijira daga Darfur, dake sansanin Iridimi a Cadi.

Tawagar farkon ta kunshi 'yan gudun hijira 53 daga sansanin MDD dake kasar Cadi, cikin mutane dubu dari uku dake sansanoni 12 dake karkashin kulawar MDD

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD tace tawagar farko da 'yan gudun hijira daga yankin Darfur na Sudan da suke zaune a Cadi, su 53, sun koma gidajen su a arewacin Darfur da suka tsere suka bari fiyeda shekaru 10 da suka wuce, kamar yadda rahoton Lisa Schlien daga Geneva yake cewa.

Hukumar ta bayyana fatar ganin komawar wannan tawaga zata zaburadda dubban 'yan gudun hijira daga yankin a kashin kansu su fara komawa gida.

Hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD tace yanayin tsaro a yankin ya inganta sosai, ba kamar a shekara ta 2003, lokcin da 'yan tawaye suka fara yakar gwamnatin ta Sudan ba.
Tawagar ta 'yan gudun hijirar su 53, da suka baro sansanin 'yan gudun hijira dake Iridimi ranar Asabar, suna daga cikin 'yan gudun hijira dubu dari uku daga yankin Darfur, wadanda ahalin yanzu suke zaune asansanoni 12 karkashin kulawar MDD, da wadanda gwamnati ta kafa.

Ahalinda ake ciki kuma, hukumar kula da 'yan ci rani da gudun hijira ta kasa da kasa, ta bayyana damuwa ba zata iya kare 'yan gudun hijira 'yan Rohingya da suke Bangladesh, daga ruwan sama kamar da bakin kwariya da ake tsammanin zai fatattaki yankin cikin kwanaki masu zuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG