Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijira Na Kauracewa Sansanonin Da Ke Kusa Da Najeriya


Najeriya 'yan gudun hijira a Nijar, Mayu 6, 2015.

Daruruwan ‘yan gudun hijira na cikin gida a arewacin kasar Kamaru, suna kauracewa sansanan dake kusa da kan iyaka da Najeriya, bisa ga cewarsu, yanzu rayuwarsu na cikin hadari, biyo bayan hare haren kunar bakin wake da aka kai, yayinda gwamnati ke kira da a kwantar da hankali.

Kimanin mutane goma sha suka mutu da suka hada da ‘yan kunar bakin waken, talatin kuma suka ji raunuka.

Samari Bakassia wani magidanci dan shekaru arba’in wanda matarsa ta rasu a harin, yace ya kauracewa sansanin da jaririyarsa ‘yar wata biyu sabili babu tabbacin tsaro.

Yace suna cikin dimuwa, yanzu suna dogara ga Allah ya cecesu daga hannun ‘yan ta’addan.

Gwamnatin kasar Kamaru tace kimanin mutane dari da hamsin suka kauracewa sansanin da aka tsugunar da ‘yan kasar Kamaru dari biyar, dake gudun mayakan Boko Haram.

MDD tayi kiyasin cewa, kimanin ‘yan kasar Kamaru dubu maitan suka rasa matsugunansu sakamakon tashin hankalin Boko Haram, kashi saba’in cikin dari kuma kanananan yara ne.

Facebook Forum

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG