Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijira Sun Yi Zanga-Zanga A Lesbos


'Yan gudun hijira masu zanga-zanga a Lesbos
'Yan gudun hijira masu zanga-zanga a Lesbos

‘Yan gudun hijirar da ke fusace sakamakon gobara da ta lashe sansanin sun bukaci barin Lesbon da ke tsibirin Girka a jiya Assabar, a yayin da hukumomi suka bude sababbin tantuna, kana kuma shugabannin Turai sun sha kiraye-kirayen tsgunar da karin wadanda suka rasa muhallansu.

Fiye da mutane 12,000, mafi akasari daga nahiyar Afirka da Afghanistan suke kwana a cikin matsanancin hali, tun sa’adda wutar gobara ta kone daukacin sansanin ‘yan gudun hijira na Moria da ke da dimbin cunkoson jama’a a farkon wannan makon.

Wasu mazauna sansanin na dauke da cutar COVID-19, lamarin da ya kara haifar da fargabar yiwuwar yaduwar annobar.

Daruruwan ‘yan gudun hijiran sun tattaru cikin matsanancin zafin rana suna rera taken “neman ‘yanci” da “barin sansani”, a daidai lokacin da manyan motoci suke share fili domin kakkafa tantuna.

Zanga-zangar 'yan gudun hijira a Lesbos
Zanga-zangar 'yan gudun hijira a Lesbos

Wasun su sun rirrike kwallaye masu rubuce da sakwanni, da suka hada da “Ba ma bukatar komara mawuyacin wuri irin Moria” da kuma “Shin kina jin mu Merkel?”, suna yin kiran ga shugabar Jamus.

‘Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa na dan gajeren lokaci sa’adda wasu daga cikin masu zanga-zangar suka yi yunkurin yin maci akan titin da ya nufi babbar tashar jiragen ruwan tsibirin ta Mytilene, hanyar da ‘yan sandan suka toshe a yayin da ake ci gaba da aikin kakkafa sababbin tantuna a kusa.

'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa ga masu zanga-zanga a Lesbos
'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa ga masu zanga-zanga a Lesbos

Mataimakin shugabar Jamus Olaf Scholz, ya yi kira ga kasashen Turai da su karbi karin ‘yan gudun hijira, to amma rashin cimma wata yarjejeniya akan haka ya kawo cikas, kamar yadda shugaban Austria Sebastian Kurz ya bayyana, inda ya ce shi ba zai karbi karin ‘yan gudun hijira ba a kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG