Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan gudun hijirar Liberiya da ke Ghana ba sa son komawa gida


Shugaban Ghana John Evans Atta Mills
Shugaban Ghana John Evans Atta Mills

Rahotannin dake fitowa daga kasar Ghana na cewa mafi yawan ‘yan gudun hijirar Liberia dake zaune a Ghana suna kin yarda da a maida su kasarsu

Rahotannin dake fitowa daga kasar Ghana na cewa mafi yawan ‘yan gudun hijirar Liberia dake zaune a Ghana suna kin yarda da a maida su kasarsu duk da kuratowar da wa’adin karshen aiki da dokar da ta basu damar zama a matsayinsu na ‘yan gudun hijira a Ghana.

Tetteh Padi, shine babban jami’in dake kula da ‘yan gudun hijirar Liberia a Ghana yace talatin ga watan Yuni aka baiwa ‘yan gudun hijirar Liberia da su kammala kimtsawa domin ranar ce wZA’adin kasancewarsu ‘yan gudun hijira ke karewa, snanan ya kara da cewa:

Matsalar ita ce, ‘yan gudun Hijirar sun gudu ne daga kasarsu Liberia, saboda yakin basasa, anyi sa’ar kawo karshen yakin basasar. Kuma tun daga lokacin kawo karshen yakin basasar an gudanar da zaben fallen daya bisa salon demokuradiyya, an kuma sami nasarar zaben cikin ‘yanci da walwala don haka yanzu nakwai Gwamnatin farar hula a Liberia, ke nan ‘yan gudun hijirar nada ‘yancin komawa gidajensu suci gaba da rayuwarsu.

Yanzu an shafe kusan shekaru ashirin da samar da dokar baiwa ‘yan gudun hijirar Liberia iznin zama a Ghana babu wata tsangwama,amma kuma aiki da wannan dokar zai kare ne a karshen watan Yuinin nan mai zuwa, don haka yanzu ake kokarin basu damar komawa kasarsu. Shin wane kokari ke nan ake yi domin shirya masu takardun Bulaguro? Babban jami’in kula da wuraren zaman ‘yan gudun hijira a Ghana gavivina Tamakloe yayi Karin bayani.

Yace ba matsala idan suna son ci gaba da zama a kasar Ghana, amma bisa ga tsarin kasa da kasa za’a amince da zama dan kasa ne idan kana rike da Fasfo na kasar da ka fito, idan dan Liberia nada fasfon na Liberia, abin yi shine jami’an Ghana su karbi fasfon din su buga masa tambarin zama dan kasa.

XS
SM
MD
LG