Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijirar Najeriya Sun Bukaci Komawa Kasarsu


'Yan gudun hijirar da suka tsere daga Najeriya zuwa jamhuriyar Kamaru sakamakon hare-haren Boko Haram, sun bukaci a mayar da su garuruwansu na asali.

'Yan Najeriya da suka tsere zuwa kasar kamaru sakamakon harin boko haram sunyi fata cewa gwamnati zata gaggata mayar dasu garuruwan su na asali.

Wakilin muryar Amurka Moki Edwin Kindzeka ya kai ziyara a sansanin yan gudun hijiran domin jin shin menene fatar su a wannan sabuwar shekarar.

Yanzu dai ana cikin bikin sabuwar shekara da kuma kirismeti

kuma haka yake ko a garin Garwa dake yankinMayo dake arewacin Cameroon a wurin da kasar tayi iyaka da Najeriya ta arewaci.

Nan ne dai wurin da ya zamo tamkar gida ga dubban jamaan Najeriya dake gudun hijira.

Maaikatar wata kungiya mai zaman kanta da ake kira da turanci World Luthern Federation, wacce kungiya ce mai gammayar kungiyoyin coci-coci na kasashen duniya har 145 dake kasashe 98, an gansu a wannan sansanin suna suna raba kyaututtuka kasna suna gudanar da adduoi da wadannan ‘yan gudun hijiran da rikicin boko haram ya rabo su da gidajen su.

Aubin Nzali na kungiyar ta WLF yace sun shirya wani shiri na musammam har na tsawon sati biyu da zai kara dankon zumunci tsakanin yan gudun hijiran da masu masaukin su.

Yace kasancewar zaman ‘yan gudun hijira a wannan wuri yayi matukar tasiri ga rayuwar masu masaukin nasu, musammam ma akan abubuwan su na more ratyuwa, wanda can dama yana tangal-tangal ne.

Yace amma kawo su wuri guda ta hanyar wannan shirin zai kara sa bangarorin biyu su kusanci juna ta hanyar zamantakewa mai maana musammam a wannan yanayi dake cike da kalubale.

Daya daga cikin wadannan yan gudun hijira dan shekaru 28 mai suna Emanuel Kaladjavi wanda ya gudo daga jihar Bornon Najeriya a cikin watan janairu na shekarar data gabata .

Yace sakamakon wannan harin na boko haram yayi hasarar dan uwansa, kana kawo yanzu baiga matar sa ba, sai yace yana murna ALLAH cikin ikon sa yasa yaga wannan sabuwar shekara cikin koshin lafiya.

Gaskiya ina mai cike da farin ciki domin ko mutane da yawaa sun mutu a cikin 2017 amma ALLAH cikin ikon say a bar mu da ran mu, gaskiya muna murnan ganin wannan sabuwar shekarar.

Emmanuel yace fatar guda ce yanzu shine yaga ya koma Najeriya inda zai saka ganawa da ‘yan uwansa .

Yace kawo yanzu abinda yake jira shine tabbaci daga gwamnatin Cameroon da na Najeriya, cewa tursasawan da suka fuskanta daga ‘yan boko haram yak au kuma yazo karshe yanzu suna iya zama cikin kwanciyar hankali.

Shi dai wannan kauyen da suke da ake kira Garwa yana nisan kilomita 5 daga sansanin yan gudun hijira na Minawao, wabnda nan ne ‘yan gudun hijira da yawan su yakai dubu 72.

A cikin shekarar 2017 mutane da yawan su yakasi dubu 12 ne suka iso wannan sansanin, wanda kuma dubbai daga cikin su sun nemi su koma inda suka fito su da kansu kamar yadda gwamnati kamaru ke cewa.

Ali Shouek wani dan shekara 41 ,ya iso wannan sansanin ne yau shekaru kunen da suka gabata , amma yace sam kawo yanzu baya tunanen komawa inda ya fito.

Yace baya son ya sake komawa cikin irin yanayin da ya baro baya musammam kuntatawa irin na ‘yan boko haram wadanda suka kai hari a kauyen sun a Attagara dake arewacin Najkeriya, inda sukakashe mutane da dama kana suka banka wa gidaje da yawa wuta, abinda ya tilasta mutane masu tarin yawa zama ‘yan gudun hijira da karfi da yaji.

Yace shi kan zaman wannan sansani yafi masa sau dubu da sake daukart kaddarar komawa gida, gidan da baya da tabbacin zaman lafiya.

Kullun muna haduwa a wuri guda muna gudanar da ibadar mu wata sa a kuma tundaga sha biyun rana muke faraway, munazuwa wurare muna rawa muna waka muna zaman mu cikin raha da annashuwa har ma muna yiwa junakyauta.

Gwamnatin kasar Cameron dana Najeriya da kuma hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD su ukkun sun cimma yarjejeniyar ganin an mayar da yan gudiun hijirar garuruwan su amma kuma tare da basu zabi idan suna son hakan amma kuma aiwatar da hakan tun a cikin watan Maris na shekarar data gabata,Aneth Mbane na kungiyar nan ta WLF tace gudanar da wannanzi zamo idan yan gudunhijirar na bukatar komawa garuruwan nasu ne bba wai a tilasta musu ba.

Wannan yarjejeniyar da kasar Cameroon tasa wa hannuda Najeritya da hukumar gkulada yan gudu hijira anyi da niyyar daidaita alamuran yan gudun hijiram

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG