Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan gwaggwarmaya sun zargi gwamnati da kashe mutane 90 a Siriya


Gawarwakin wadanda aka kashe a Siriya

'Yan gwaggwarmaya a kasar Siriya sun ce an kashe sama da mutane 90 da suka hada da kananan yara

Yan gwaggwarmayar kasar Siriya sun bayyana jiya asabar cewa, an kashe sama da mutane casa’in da suka hada da kananan yara da dama cikin sa’oi 24 a wani hari da dakarun gwamnati da mayaka suka kai a wani kauye dake kusa da birnin Homs.

Damascus bata musanta kisan ba, sai dai ta dorawa wadanda ta bayyana a matsayin ‘yan ta’adda, alhakin asarar rayukan da ake yi tun lokacin da aka fara zanga zangar kin jinin mulkin shugaba Bashar al-Assad watanni 15 da suka shige.

Wata tawagar masu sa ido karkashin jagorancin janar Robert Mood ta isa kauyen jiya asabar domin gudanar da bincike kan kisan. Janar din yayi allah wadai da wannan “kazamin bala’n” ya kuma ce masu gani da idon sun kirga gawarwakin kananan yara ‘yan kasa da shekaru goma guda 32 yayinda aka kashe sama da manyan mutane 60.

Wani hoton bidiyo ya nuna dangi suna binne gawarwakin wadanda aka yiwa kisan gillan ranar jumma’a. Shaidu sun ce an fara kisan ne lokacin da dakarun gwamnati suka bude wuta a kauyen bayan sallar jumma’a. Bisa ga cewarsu, an kashe wadansu mutanen yayin bude wutar yayinda wadansu kuma suka rasa rayukansu a harin da wata kungiya dake goyon bayan gwamnati da ake kira Shabiha ta kai.

Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon da manzon Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan larabawa a Siriya Kofi Anan, sun yi Allah wadai da tashin hankalin. Suka kuma bayyana hare haren a matsayin abin takaici da mummunan laifi da ya shafi amfani da iko fiye da kima.

Dubban masu makoki sun fito jiya asabar a Aleppo birni mafi girma a kasar Siriya, domin gudanar da zanga zangar kin jinin harin wanda ya kawo wani sabon cikas a kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma karkashin jagorancin Kofi Anan. Kimanin maso gani da ido na Majamisar Dinkin Duniya 300 ne suke Siriya a halin yanzu, domin ganewa idonsu lamarin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG