Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan gwagwarmaya sun zargi Siriya da kai sabbin hare-hare


Cigaba da zanga-zanga a Siriya

‘Yan rajin kare hakkoki sun zargi dakarun gwamnatin Syria da barin

‘Yan rajin kare hakkoki sun zargi dakarun gwamnatin Syria da barin wuta kan birnin Homs na yankin tsakiyar kasar, wanda hakan ya tayar da wata sabuwar ayar tambaya game da makomar tsagaita wutar kasar da tun dama ke tangal-tangal.

Mazauna birnin na Homs sun ce an fara kai masu harin ne tun da tsakar dare har zuwa safiyar yau Asabar. Kungiyar sa ido kan hakkoki bil’adama a Syria mai hedikwata a Burtaniya ta ce har yanzu ta na jiran bayanai game da wadanda abin ya rutsa da su.

Bayanin kai harin ya zo ne a daidai lokacin da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ke shirin kada kuri’a kan batun tura wani karamin rukunin soji da zai sa ido kan batun kiyaye yarjajjeniyar tsagaita wutar.

‘Yan adawa dai sun yi ta zanga-zanga a wuraren da aka saba yi a fadin Syria. ‘Yan rajin kare hakkoki sun ce dakarun gwamnati sun yi ta barin wuta kan masu zanga-zanga a wurare da dama, ciki har da Hama, inda nan ne abin ya fi karfi.

Da gwamnatin Syria ta ce za ta mayar da martani ne kawai idan ‘yan bindiga su ka kai mata hari. To amman dan gwagwarmayar adawa a Hama mai suna Samir a-Husain ya gaya wa Muryar Amurka cewa an kai harin na jiya Jumma’a ne ba tare da wata tsangwama ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG