Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gwagwarmayar Islama a Mali Sun Cigaba da Tattaunawa da 'Yan Tawayen Asbinawa


Dambarwar siyasa a Mali
Dambarwar siyasa a Mali

Wata kungiyar kishin Islama a kasar Mali ta bada sanarwar amincewa

Wata kungiyar kishin Islama a kasar Mali ta bada sanarwar amincewa da fara tattaunawa da wakilan mayakan ‘yan tawayen Abzinawan kasar Mali kan batun kirkiro sabuwar kasar da zata rika aiki da shari’ar Islama a yankin Arewacin kasar Mali.

A tattaunawar suka yi da wakilin muryar Amurka (VOA), jami’an kungiyar dake da alaka da al-qaida ta Ansar Dine, yau Asabar take tabbatar da sahihancin rahoton amincewa sake zaunawa domin tattaunawa da kungiyar ‘Yan tawayen Abzinawan Mali ta MNLA.

Haka na faruwa ne kwana guda bayan wani babban jigon kungiyar ‘yan tawayen Abzinawa ya bada sanarwar ballewa daga gungun masu neman kafa tasu kasar mai zaman kanta. Ya bada hujjar cewa yafi son ci gaba da kasancewa a sahun ‘yan ba ruwan mu.

XS
SM
MD
LG