Kusan mako biyu bayan kisan gillar da aka yi wa wani fitaccen mawaki a kasar Habasha, dubban ‘yan kasar mazauna Amurka da kuma wasu kasashen sun nuna jimamin mutuwar mawakin ta hanyar gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna fushinsu ga hukumomin Addis Ababa.
A birnin Minneapolis da ke Minnesota, jihar da aka fi samun ‘yan kabilar Oromo, mutum akalla 1,500 suka datse wata babbar hanya har sama da sa’a guda a karshen makon da ya gabata.
Mutuwar mawaki Hachalu Hundessa dan shekara 34 da haihuwa, wanda aka harbe har lahira a Addis Ababa a ranar 29 ga watan Yuni, ta sa ‘yan kabilar ta Oromo sun hada kai domin nuna adawarsu ga Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed.
A farkon watannan nan, a yayin wata hira da Muryar Amurka ta yi da Farfesa Henok Gabisa na jami’ar nazarin aikin Shari’a da ake kira Lee University, ya kwatanta wake-waken Hachalu a matsayin na “juyin juya hali.”
An dai yi ta zanga-zanga a sassan kasar Habasha bayan kisan mawakin, wacce ta sa aka yi fito-na-fito da jami’an tsaro.
Hukumomin kasar sun ce an kama kusan mutum 5,000 sannan wasu 239 sun mutu sanadiyyar zanga-zangar. Lamarin ya kai ga har sai da aka katse hanyoyin sadarwar yanar gizo a wani mataki don kwantar da tarzomar.
Facebook Forum