Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Houthi Sun Kwace Fadar Shugaban Yemen


Magoya bayan 'yan Houthi

'Yan tawayen Houthi da kawayensu sun kutsa birnin Arden inda suka kwace fadar shugaban kasar Yemen

Jami’an kasar Yemen sun ce ‘yan tawayen kungiyar Houthi ta ‘yan Shia’ da abokan kawancensu sun yi ta bude wuta har suka sami kutsawa tsakiyar Aden jiya Alhamis suka kwace fadar shugaban kasa a birnin mai tashar sufurin jiragen ruwa.

‘Yan tawayen sun yi ta kutsawa cikin Aden ‘yan kwanakin nan, yayinda gumurzun ya tilastawa dakarun shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi dake da goyon bayan kasashen ketare, arcewa daga Aden makon da ya gabata.

Kwace Aden da suka yi, birni karshe da ya rage a hannun dakarun dake goyon bayan Mr Hadi, ya zama wata koma baya ga rundunar hadin guiwa da kasar Saudi Arebiya ke jagoranta, wadda ta shafe sama da mako guda tana kai hare hare ta sama a Yemen

A wani taron manema labarai a Riyadh babban birnin kasar Saudiya, wani jami’in tsaron kasar yace ya hakikanta cewa, kawo yanzu, kura ta lafa a birnin.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG