Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Magana Da Yawun Fadar White House Ya Ajiye Aikinsa


Sean Spicer
Sean Spicer

Mai magana da yawun fadar White House Sean Spicer ya yi murabus.

Yau jami’in watsa labaran fadar shugaban Amurka ta White House, Sean Spicer ya yi murabus daga aikinsa.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa kudurinsa na ajiye aiki na da alaka da nadin sabon daraktan yada labarai na fadar shugaban kasa Anthony Scaramucci. Inda suke cewa Spicer ya mika takardar murabus din sa ne jim kadan bayan da aka nada sabon daraktan.

A tarukan manema labarai da yake gudanarwa a fadar shugaban kasa Sean Spicer ya janyo hankulan masu kallon talabijin da kafofin sada zumunta. A baya bayan nan dai mataimakiyar Spicer ce ke gudanar da tarukan.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG