Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasa Sun Fara Bayyana Matsalolin Dake Bukatar Daukin Gaggawa Daga Shugabanni Masu Zuwa A Badi


Yan Siyasar Najeriya Sun Garkame Kofofin Shiga Majalisar Dokoki.
Yan Siyasar Najeriya Sun Garkame Kofofin Shiga Majalisar Dokoki.

Bayan kammala zabubbukan fidda gwani da jami’iyyun siyasa a Najeriya suka yi, al’ummar kasar sun fara tofa albarkacin bakinsu kan bukatun da suke so wadanda suka sami shugabanci a zaben shekara ta dubu biyu da ishirin da uku, su fuskanta, don kawo sauyi mai inganci a rayuwarsu.

A Jahar Filato, wasu da muryar Amurka ta zanta da su sun bayyana cewa harkokin ilimi, rashin ayyukan yi, matsalolin shaye-shaye da inganta rayuwar al’umma na daga cikin dimbin bukatu na gaggawa da gwamna da zai karbi mulki zai magance.

Malama Bilkisu Umar tace suna bukatar ‘ya’yansu su sami ilimi mai inganci don tallafa wa kansu da zuri’ar su.

Jabir Abdulrazak yace rashin aikin yi ya sanya wassu matasa shiga shaye-shaye da wassu harkoki marasa fai’ida

Barista Caleb Mutfwang dake takarar gwamnan Jahar Filato a jami’iyyar PDP yace zai magance matsalolin tsaro don samar da kayayyakin more rayuwa ga al’umma.

Shima ‘dan takarar gwamnan Jahar Filato a APC, Farfesa Nentawe Yilwatda yace zai kafa gidauniya don samun kudaden da zai magance rashin tsaro da samadda ci gaba.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

XS
SM
MD
LG