Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Bude Taron Karawa Juna Sani Na Kwana Uku A Jihar Filato

Rundunar Sojin Najeriya Ta Bude Taron Kwana Uku Na Karawa Juna Sani A Jihar Filato

Rundunar sojin Najeriya ta ce zata ci gaba da horar da jami’anta don tinkarar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta da zummar magance su.

PLATEAU, NIGERIA - Hafsan Hafsoshin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya bayyana haka ne yayin bude wani taron karawa juna sani na kwanaki uku a runduna ta uku dake Jos a Jihar Filato.

Taron mai taken ‘inganta karfin sojojin Najeriya don tunkarar kalubalen tsaro na zamani a cikin yanayi na hadin gwiwa da rawar da manyan shugabanni ke takawa’, ya hado kan sojoji masu mukamin janar-janar da wadanda ke jiran mukaman janar da kwamandojin sojin daga Arewacin Najeriya.

Rundunar Sojin Najeriya Ta Bude Taron Kwana Uku Na Karawa Juna Sani A Jihar Filato
Rundunar Sojin Najeriya Ta Bude Taron Kwana Uku Na Karawa Juna Sani A Jihar Filato

Hafsan Hafsoshin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ce taron na karawa juna sani kafa ce ta yadda manyan sojojin za su kara fahimtar hanyoyin gudanar da ayyukansu.

A hirar shi da wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji, Hafsan hafsoshin ya ce taron na karawa juna sani kafa ce ta yadda manyan hafsoshin za su kara fahimtar hanyoyin gudanar da aikin su da cike gibin da su ke samu.

Saurari rahoto cikin sauti daga Zainab Babaji:

Rundunar Sojin Najeriya Ta Bude Taron Kwana Uku Na Karawa Juna Sani A Jihar Filato
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

XS
SM
MD
LG