Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Indonesia Sun Kada Kuri'a A Yau


A yau Laraba ne ‘yan kasar Indonesia suka fara kada kuri’a wanda ya zama zabe mafi girma da za’a gudanar a cikin rana guda.

Akalla mutane miliyan 193 suka cancanta su taka rawa a cikin zaben da zai fitar da wanda zai yi shugabancin kasar da ta fi yawan musulmai a duniya.

Mafi akasarin ra’ayin mutane da aka lissafa sun nuna Widodo na gaba. Amma Prabowo ya fada wa manena labarai da yammacin jiya Talata cewa yana sa ran cin zabe da kashi 63 a cikin 100.

‘Yan kasar Indonesia za su zabi mataimakin shugaban kasa, ‘yan majalisar tarayya, na yankuna da na karkara a cikin ‘yan takara 20,000.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG