Accessibility links

Yan kasar Kenya sun yi karar Ingila sabili da gallaza masu a tarzonar 1950


Babban alkalin kasar Kenya Willy Mutunga

Wadansu dattijai ‘yan kasar Kenya sun bayyana a gaban wata kotun ingila suna neman diyyar akubar da sojojin Ingila suka gana musu

Ranar Alhamis ta makon jiya wasu dattijai uku ‘yan kasar Kenya suka bayyana a gaban wata kotun ingila suna neman diyya saboda irin akubar da sojojin Ingila suka gana musu a wajajen 1950 lokacinda ake boren kyamar mulkin mallakar ingila da aka lakabawa sunan Mau Mau.

Lauyan mutanen yace cikin akubar da aka gana musu har da dandake su, da kuma lalata dasu, da lakada musu duka lokacin da ake tsare da su.

Mutanen uku suna neman Ingila ta nemi gafara san nan ta samar da kudade domin kulawa da wadanda sojojin mulkin mallakar suka gallazawa.

An kiyasta cewa an kashe akalla mutane da ya kama daga dubu 10 zuwa dubu 90 lokacinda ‘yan kasar Kenya suka tada kayar baya kan salon mulkin mallakar turawan Ingila.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG