Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Laberiya Na Zabe A Karo Na Biyu Tun Bayan Yakin Kasar


Ma-Fanta Konneh 'yar shekaru 60 na kada kuri'ar ta, ta zaben shugaban kasa a wata makaranta a Kendeja, birnin Monrovia, kasar Laberiya ranar talatar nan 11 ga watan oktoba

'Yan kasar Laberiya sun fita zabe cikin ruwan sama a yau Talata

‘Yan kasar Laberiya sun fita zabe cikin ruwan sama a yau talata, wannan ne karo na biyu da ‘yan kasar ke zabe tun bayan yakin basasar da aka yi shekaru 14 ana yi.

Dimbin mutane sun isa rumfunan zabe tun da tsakar dare domin su zama na farkon kada kuri’un su a zaben shugaban kasar wanda ake fafata takara sosai a kai.

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf na fuskantar abokan takara masu yawa a neman wa’adin mulkin ta na biyu, bayan wasu ‘yan kwanaki kalilan da samun kyautar yabon Nobel a fannin zaman lafiya.

Ta na karawa da wasu ‘yan takara fiye da 12, kuma takarar da ta fi zame ma ta cikas ita ce ta su George Weah tauraron wasan kwallon kafa.

A zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar dubu biyu da biyar George Weah shi ne ya zo na biyu, amma a wannan karo takarar mataimakin shugaban kasa ya ke yi tare da Winston Tubman wanda shi ma kamar Mrs.Sirleaf a jami’ar Harvard ya yi karatu.

‘Yan hamayya na zargin cewa shugaba Sirleaf ta kasa gyara bannar da yaki ta yiwa kasar ballantana kuma ta rage radadin talauci da rashin ayyukan yi.

Amma magoya bayan ta na cewa ta tabbatar da zaman lafiya kuma ta shafewa kasar bashin dubban miliyoyin dalolin da kasashen waje ke bin ta.

XS
SM
MD
LG