Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An gwabza mumunar fada a kasar Somaliya

洛杉矶县格伦代尔市议员和韩国裔社区代表为塑像揭幕

Mumunar fada ya gwabje a Mogadishu baban birnin kasar Somaliya a yayinda sojojin gwamnati suka yi kokarin fatattakar ‘yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab daga babar tungarsu ta karshe a birnin.

Mumunar fada ya gwabje a Mogadishu baban birnin kasar Somaliya a yayinda sojojin gwamnati suka yi kokarin fatattakar ‘yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab daga babar tungarsu ta karshe a birnin.

Mazauna arewacin birnin Mogadishu sun bada rahoton cewa sunji tashin bama bamai da karajin harbe harbe a yau litinin a yayinda sojojin gwamnati da sojojin kungiyar kasashen Afrika suke danawa zuwa sansanonin kungiyar Al Shabab.

Ana wannan fafatawa ne, bayan da, a kwanaki masu harin kunar bakin wake na kungiyar Al Shabab suka kashe mutane tamanin a wani ginin gwamnatin Somaliya. Wannan ne baban harin da kungiyar Al Shaba ta kai tun lokacin data janye yawancin mayakanta daga birnin a Watan Augusta.

XS
SM
MD
LG