Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Liberia Naci Gaba Murnan Zaben Sabon Shugaban Kasa.


Niger Elections

'Yan kasar Liberia naci gaba da murnan a babban birnin kasar ta Monrovia biyo bayan zaben sabon shugaban kasa George Weah

Cincirindon jamaa ne a babban birnin kasar Liberia wato Monrovia suke ta bukukuwa jin dadin nasarar da zababben shugaban kasar Liberia George Weah.

An zabi sabon shugaban ne da mataimakiyar sa Jewel Howard Taylor, biyo bayan zaben ranar 26 ga wannan watan da aka yi a kasar.

A sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar jamiaiyyar Geoge Weah ta Coaliation For Democratic Change ta samu kuri’u kashi 61.5, yayin da mataimakin shugaban kasa Joseph Boa-kai na jamiyyar Unity Party ta samu kashi 38.5.

Shidai Weah dan shekaru 51 ne, tsohon dan wasan kwallon kafa ne da yayi suna a wasan na kwallon kafa kuma ya shiga harkokin siyasa ne bayan yayi murabus daga buga wasan na kwallo, a cikin shekarar 2002 ya zama sanata.

A cikin watan gobe na sabuwar shekarar ce zai kama ragamar mulkin kasar,

Wannan ne dai karo na farko tun bayan shekaru 70,da kasar ta Liberia zata yi musayar gwamnati daga farar hula zababbiya zuwa wata irin ta.

Shugaba Mai barin gado wacce ita ce mace ta farko a Africa, Ellen Johnson Sirleaf wadda tayi waadi biyu na mulkin kasar zata sauka daga kan karagar mulki.

Ta dai mulki kasar ce bayan data fito daga yakin basasa kana kuma daga bisani tazo tayi fama da cutar ebola mai kissa kaf daya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG