Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Rwanda Sun Zabi Tazarcen Shugaba Paul Kagame


Shugaban Rwanda Paul Kagame

Shugaban hukumar zaben kasar Ruwanda Charles Munyaneza ya bayyana cewa, wani bangare na sakamakon zaben da ake tattarowa ya nuna cewa ‘yan kasar sun zabi yarda da tsarin mulkin da zai bawa shugaba Paul Kagame damar yin tazarce.

Masu zaben raba gardama a Rwanda sun zabi canza kundin tsarin mulkin kasar da zai bawa Shugaba Paul Kagame damar yin tazarcen mulkin kasar har nan da 2034 idan ya tsallake zaben kasar da za a yi bayan gama wa’adinsa na 2017.

Babban Sakataren hukumar zaben kasar ne ya bayyana haka a yau da yake magana da manema labarai Kigali babban birnin kasar. Ya ce an yi zaben cikin kwanciyar hankali.

Inda ya fadi cewa masu kada kuri'a Miliyan shida da Dubu Dari da Hamsin da Biyar ne suka zabi amincewa akan wadanda basu amince ba su Dubu Dari da Dari Takwas da Sittin da Uku.

A bisa dokar da take kasa dai tana bukatar ya sauka a karshen shekara ta 2017, amma idan ya haye wannan zaben raba gardamar, zuwa cin zabe, to zai ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2034.

Tun dai shekara ta 2000 Kagame dan shekaru 58 yake kan mulkin kasar, bayan jagorantar sojojin da suka kawo karshen yakin basasar kasar tsakanin ‘yan kabilar Hutu da Tutsi.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG