Accessibility links

'Yan Kasuwa A Taraba Na Korafin An Mayardasu Saniyar Ware


Yaki da cututuka aTaraba

Wasu 'yan kasuwa a jihar Tara sun kai korafinsu wa gwamnan jihar cewa an mayardasu saniyar ware

'Yan kasuwa a jihar Taraba sun yi korafin cewa an mayardasu saniyar ware domin ba abun da gwamnati ta yi na inganta da habaka harkokin kasuwanci a jihar.

'Yan kusawan sun yi jerin gwano zuwa gidan gwamna domin su shaida masa cewa ana son a mayardasu saniyar ware a harkokin jihar. Shugaban 'ayn kasuwan Alhaji Jamande Adamu ya ce suna bukatar a habaka harkar kasuwanci da noma da kiwon lafiya. Yayin da yake jawabi shugaban ma'aikata a gidan gwamnati Injiniya Ahmed Yusuf Gamaliel ya ce gwamnati bata manta da 'yan kasuwan ba. Ya ce bunkasar 'yan kasuwa shi ne alfaharin gwamnati. Idan babu su gwamnati ba zata zauna ba.

Yankunan karkara nada rawar da suke takawa wajen cigaban kasuwanci musamman ma a jihohon arewacin Najeriya. Dalilin da ya sa ke nan gwamnatin jihar ta fi bada fifiko da gina hanyoyin karkara. Kwamishanan ayyuka ya ce kowace karamar hukuma an yi mata hanyoyin kilomita hudu kuma ayyukan na cigaba.

Jihar Taraba nada manyan kasuwoyi na albarkatun noma da dabbobi. Idan aka inganta hanyoyi to fa jihar zata anfana matuka.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

XS
SM
MD
LG