Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Korea Ta Kudu Sun Nace Sai Park Ta Yi Murabus


Dandazon Masu Zanga zanga a Koraea ta Kudu

Daruruwan ‘yan kasar Korea ta Kudu ne suka yi gangami a birnin Seoul a daren jiya Asabar, a wani bore da ba’a taba ba gani ba, tun da aka fara kira ga shugabar kasar Park Guen-hye ta sauka daga mulki.

Dumbin masu zanga zanga ne suka taru a karshen mako na biyar a jere a cikin birnin na Seoul, suna neman shugabar ta mika wuya, bayan abin fallasar da ake zargin Geun-hye ta aikata a farkon shekarar nan.

‘Yan sanda sun ce akalla mutane dubu 270 ne suka fita wannan gangami, amma kuma wadanda suka shirya taron sun ce mutane miliyan-daya-da-rabi ne suka fita.

An dai girke kusan ‘yan sanda dubu 25 domin dakile aukuwar hare-hare, da kuma hana masu boren yin tattaki zuwa Fadar Shugabar kasan na Blue House.

Ana dai zargin shugabar da taimakawa wata kawarta, mai suna Choi-Soon-sil da yin katsalandan a harkokin gwamnati, da kuma karbar kudade a hanun kamfanonin kasar domin ta tara dukiya.

XS
SM
MD
LG