Daya daga cikin shugabannin kungiyar tace sun zabi canji a zaben 2015 kuma sun ga canjin a yaki da 'yan ta'ada ba koma bayan da aka samu na cinye kudin makamai a gwamnatin da ta shude ba, inji Maureen Kaburuk yayinda da take bada rahoton ziyarsu zuwa dajin Sambisa.
'Yan kungiyar a karkashin shugabancin Oby Ezekwesili sun bi tawagar jami'an tsaro a jirgin sama na sojoji zuwa dajin dake arewa maso gabas inda suka samu yin shawagi kan fadin dajin Sambisan.
Bayan jawabansu Oby Ezekwesili tace babu shakka sun kara gamsuwa da yadda dakarun Najeriya suka yi tsayin daka na ganin sun kawar da 'yan Boko Haram da kwato sauran 'yan matan Chibok dari da casa'in da biyar.
Kungiyar ta nuna kwarin gwuiwa da irin shirin da sojojin keyi na kakkabe duk 'yan ta'adan tare da kwato duk wadanda ake tsare dasu a dajin.
'Yan kungiyar sun ga aikin da sojojin suka yi tun daga Yola jihar Adamawa zuwa dajin Sambisa mai tsawon kilomita dubu sittin da ya ninka Legas har sao takwas har zuwa cibiyar yaki dole da Boko Haram dake Maiduguri.
Dr Manasa Allen na cikin tawagar. Yace cikin dajin wajejen "camp zero" har yanzu sojoji na ganin tafiyar mutane kuma suna bincike sai sun gama sannan za'a gane ko nan ne 'yan matan suke ko kuma wasu ne daban.
Dangane da zargin da gwamnatin Buhari tayi cewa a gwamnatin da ta shude an sace kudin sayen makamai, Dr Allen yace wannan gwamnatin ta magance lamarin. Sun gano cewa a da idan sojoji nada abu daya yanzu suna da hudu kuma kudin da aka basu na sayen makamai bai kai kashi daya cikin goma ba da aka ba sojojin a tsohuwar gwamnatin kasar.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.