Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Kungiyar Kwadago Ta NLC Da UTC Sun Katse Shige Da Fice A Filin Jiragen Sama Na Abuja


Zanga-zangar NLC
Zanga-zangar NLC

A yau Alhamis, harkokin zirga- zirgar jiragen sama a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja sun tsaya cik yayin da mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC suka kaddamar da zanga-zangar tare da rufe kofar shiga filin jirgin.

Zanga-zangar ta samo asali ne daga harin da aka kaiwa shugaban NLC, Mista Joe Ajaero, a jihar Imo, wanda ya sa kungiyoyin suka mayar da martani a fadin kasar.


'Yan kungiyar sun isa harabar filin jirgin da misalin karfe 8:58 na safe, wanda hakan ya kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Zanga-zangar NLC
Zanga-zangar NLC

Bukatarsu ta farko ita ce dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Owerri, babban birnin jihar Imo, wanda ya haifar da cikas ga daruruwan fasinjojin da suka makale a kan hanyar.


Kungiyoyin NLC da TUC sun kuma sanar da fara yajin aikin a illahirin fadin kasar daga ranar Talata 14 ga watan Nuwamba, inda suka ce rikicin da ake yi da gwamnatin jihar Imo shi ne babban dalilin daukar wannan mataki.


Kokarin da masu zanga-zangar suka yi na samun damar shiga filin jirgin ya gamu da tirjiya daga jami’an soji da ke tsare da kofar shiga harabarar tashar filin jirgin saman, lamarin da ya kai ga toshe hanyoyin shiga da fita da mambobin kungiyar suka yi.

Zanga-zangar NLC
Zanga-zangar NLC

Sakamakon haka, zirga-zirgar ababen hawa a bangarorin biyu na filin jirgin ya yi matukar wuya, lamarin da ya tilasta wa matafiya yin tafiya da kafa don isa cikin tashar jirgin saman.


A tattaunawar da wakilin Muryar Amurka yayi ta wayar tarho da daya daga cikin fasinjojin da lamarin ya rutsa dasu, Malam Lawal Ibrahim, dan kasuwa da zai koma Kano don cigaba da harkokin kasuwancin sa, ya bayyana yadda fasinjoji da jirginsu zai tashi da safe suka rinka tikar tafiya mai tsawo har cikin tashar saboda toshe hanyar da mambobin kungiyar NLC da TUC suka yi.

Zanga-zangar NLC
Zanga-zangar NLC

Batun ya dauki hankali a Manhajar X, inda mutane da dama suka rika bayyana mabanbantan ra’ayoyi.

Kotosia mai dauke da marikin @Kotosiafaze ya ce “An kara man fetur daga 185 zuwa 700 ba tare da an tuntubi NLC ba suka yi shiru, yunwa a duk fadin kasa amma NLC ta yi shiru, anyi magudin zabe NLC ta yi shiru, amma sai yanzu da ‘yan sanda suka lakada wa shugabansu duka zasu fara aiki?
Wanene a zahiri yake jin zafin ra'ayinsu yanzu? Sama da mako guda kenan babu haske a Owerri, shin Gwamna yana jin haka? Har yanzu ’ya’yan kungiyar NLC ne ke sayan mai 700 domin kasuwancinsu da gidajensu, ‘ya’yansu ne da ke IMSU da sauran makarantu a Owerri da na gani a daren jiya dauke da jarkoki a cikin gari suna neman ruwa ba yaran Hope Uzodimmas ba ne. . Duk wani abu da NLC za tayi wanda ba’a matakin kasa ne ba babu wani tasiri da zai yi…...”

Bisa dukkan alamu ‘yan Najeriya da dama sun fara gajiya da irin salon da kungiyoyin kwadagon kasar ke dauka wajen nuna rashin amincewar su ga matakan gwamnati wadanda ke iya kawo matsi a harkokin yau da kullum na kasar, babu shakka akwai bukatar samo sabbin hanyoyi don magance matsolili da kalu balen da ake fuskanta musamman a fagen matsin tattalin arziki a Najeriya.

~ Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG