Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kwanton bauna Sun Kashe 'Yan Sanda 5 A Dallas


'Yan sandan birnin Dallas dake Jihar Texas sun ce an kama mutane uku, na hudunsu kuma ya mutu, sa'o'i da dama a bayan da 'yan kwanbton-bauna suka kashe 'yan sanda biyar a wani hari lokacin da ake yin zanga-zangar lumana.

Magajin garin birnin na Dallas, yace wasu 'yan sanda bakwai da fararen hula biyu sun ji rauni a wannan lamarin.

An yi ma 'yan sandan kwanton-bauna cikin daren alhamis a lokacin da ake zanga-zangar nuna rashin jin dadin kashe wasu bakaken fata guda biyu da 'yan sanda fararen fata suka yi a jihohin Minnesota da Louisiana.

Har yanzu ana killace da wasu titunan tsakiyar birnin Dallas a yayin da 'yan sanda ke binciken wannan harin, wanda shi ne mafi muni da aka kai kan jami'an tsaro tun bayan hare-haren ta'addanci na ranar 11 ga watan Satumbar 2001.

Shugaba Barack Obama na Amurka, ya bayyana wannan kwanton bauna a zaman "mummunan abin kyama" a kan jami'an dake gudanar da ayyukansu. A lokacin da yake magana daga birnin Warsaw a kasar Poland wurin taron kungiyar kawancen tsaro ta NATO, shugaba Obama yace 'yan sanda na gudanar da ayyuka masu matukar wuya, kuma wannan farmaki da aka kai musu misali ne na irin mummunan hatsarin da suke fuskanta kullum.

Babban jami'in 'yan sandan birnin Dallas, David Brown, yace maharan da aka kama ba su bayyana dalilinsu na kai hari a kan jami'an 'yan sandan ba.

XS
SM
MD
LG