Jam'iyyar PDP ta zama jam'iyya ita kadai dake rike da majalisar dokokin jihar Adamawa.Kakakin majalisar Ahmed Umaru Sintiri yace duk dayake akwai kyakyawar dangantaka tsakaninsu da gwamnan jihar amma su suna nan daram a cikin jam'iyyar PDP. Yace wadanda suke APC da yanzu sun amince da tafiyar PDP sun dawo. Yanzu babu dan adawa a majalisar. Yace gwamna abokin aikinsu ne. Shi ma a karkashin PDP aka zabeshi.
Da wakilin Muryar Amurka ya tambayi kakakin cewa abun da suka yi shin ba wata hanya ba ce ta shirin tsige gwamnan jihar kamar yadda wasu ke zargi. Sai yace shekara daya ce kawai ta rage kafin a yi zabe sabili da haka shi baya ganin zasu gagara tafiya tare. Yace jam'iyyar PDP mai bin doka ce sabili da haka ba zata nemi su tsige gwamnan ba.
A martanin da kusoshin jam'iyyar APC suka bayar, mai magana da yawun jam'iyyar Ahmed Lawal mai ba gwamnan shawara akan harkokin cimma muradun karni yace canza shekar bata razanasu ba. Yace siyasa ce domin an kira 'yan majalisar zuwa Abuja inda aka basu kudi su bi ra'ayin jam'iyyar PDP. Inji Alhaji Lawal 'yan majalisar sun mayar da kansu 'yan kasuwa ne kawai. Yace ba akansu aka fara ba. An yi haka a majalisun wakilai da na dattawa.
Malam Muhammed Ismail wani mai sharhi akan harkar siyasa ya danganta canza shekar da kwadayin tsayawa takara.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.