A ‘yan shekarun bayan nan kasar ta Myanmar ta kyautata huldarta da Washington.
Yayin da hakan ke faruwa, ma’aikatar harkokin wajen Amurka na duba zabin kakaba takunkumi da suka hada da na tattalin arziki akan wasu mutane da kamfanoni da ake dangantawa da taimakawa wajen cin zarafin da ake yi wa Musulmin na Rohingya.
“Abinda da mu ke ganin yana faruwa a jihar Rakhine babban cin zarafi ne,” in ji mataimakin Sakataren harkokin wajen Amurka na yankin kudu maso gabashin Asiya, Patrick Murphy, yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka a jiya Talata, inda ya nuna taka-tsantsan wajen furta kalamansa.
A kwanan nan Murphy da Jakadan Amurka Scot Marciel, sun kai ziyara jihar ta Rakhine inda suka gani ido-da-ido abinda ke faruwa a kasar ta Myanmar.
Duk da cewa ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi nuni tare da ayyana sabbin matakan da za a dauka domin hukunta wadanda ke da hanu a wannan aika-aika, ya zuwa jiya Talata, manyan jami’an gwamnati sun ki su ayyana abinda ke faruwa ga Musulmin na Rohingya a matsayin “kisan kare dangi” kafin a bayyana cikakken nazarin da aka yi.
Facebook Forum