Yan jam’iyyar Democrat a majalisar wakilan Amurka sun turawa fadar shugaban Amurka ta White House umurnin neman takardun wasu bayanai dangane da binciken tsige shugaba trump da suke yi.
Shugabannin kwamitoci guda 3 a majalisar wakilan Amurka, sun fada a wata sanarwa cewa neman takardun na da muhimmanci saboda fadar shugaban ta ki ta tattauna ko ma ta ce wani abu game da umurnin neman takardun da kwamitocin su ka sha tura ma ta.
Haka zalika masu binciken na majalisar wakilai sun tura umurnin neman takardun bayanai akan mataimakin shugaban kasa Mike Pence game da abinda ya sani akan batun Ukraine, sun ambaci rahotannin dake cewa ta yiwu wani hadimin Pence ya ji tattaunawar da trump ya yi a watan Yuli da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, abinda akan batun yanzu ake binciken yiwuwar tsige trump.
A jiya Jumma’a da safe, Trump ya bayyana cewa yana da dama, bisa ga kundin tsarin mulkin Amurka ya yi yaki da rashawa, kalamansa na baya-baya dake bayyana dalilin da ya sa ya nemi taimakon gwamnatin wata kasa akan ta binciki abokin adawar siyasarsa.
Za ku iya son wannan ma
-
Afrilu 09, 2021
Mawakin Gambara DMX Ya Mutu
-
Afrilu 09, 2021
Dan Najeriya Da Ya Zama Kyaftin Din Jirgin Yakin Ruwan Amurka
-
Afrilu 03, 2021
An Kashe Wani Dan Sandan Ginin Majalisar Dokokin Amurka
-
Maris 31, 2021
Kakar Barack Obama Ta Rasu
Facebook Forum