Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Majalisar Wakilan Amurka Za Su Kada Kuri'ar Yiwuwar Tsige Trump


Daukacin ‘yan Majalisar wakilan Amurka za su kada kuri'a a wannan makon kan binciken da ke duba yiwuwar tsige shugaba Donald Trump, inda zai tabo batun gardamar da fadar White House ta ke yi na cewa binciken ba bisa ka’ida ake yin sa ba.

Kakakin Majalisar Wakilai Nancy Pelosi, ta saka ranar Alhamis a matsayin ranar da za a kada kuri’a, inda ta fada a cikin wata wasika da ta rubutawa takwarorinta cewa, tana son ta "kawar da duk wani shakku" game da shirin tsigewar.

Pelosi ta ce, matakin kada kuri’ar kan binciken tsige shugaban, zai "tabbatar da binciken da ake yi da kuma tsarin da ake bi wajen sauraren bahasi wanda zai zama bayyananne ga Amurkawa da kuma yadda za a mika hujjoji da aka samu ga kwamitin da ke kula da harkokin shari, wanda zai yi sharar fage ga yadda shugaban da lauyansa za su kare kansu.

Shi dai Trump da magoya bayansa ‘yan jam’iyyar Republican, sun kwatanta binciken a matsayin wanda baya bisa ka'ida, saboda ana yinsa ne cikin sirri, sannan gaba daya ‘yan majalisar ba su kada kuri’ar a yi binciken ba.

Sai dai Pelosi ta ce wannan hujja ta su “ba ta da tushe.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG