Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Masar Sun Fusata Kan Hukuncin Kotun Tsarin Mulkin Kasar

'Yan kasar Masar suke zanga zanga da tofin Allah tsine kan sojoji dake mulkin kasar.
'Yan kasar Masar suke zanga zanga da tofin Allah tsine kan sojoji dake mulkin kasar.

‘Yan kasar Masar sun fusata suka fantsama kan tintuna suna zanga kan tagwayen hukunci da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke, wadanda suka janyo rudani, kwanaki kamin kasar ta kaddamar da zaben fidda gwani.

Yau Alhamis kotun tsarin mulkin kasar ta yi watsi da wata dokar da majalisar dokokin kasar ta kafa wacce ta haramatawa jam’ai da suka yi aiki zamanin mulkin tsohon shuugaban kasar Hosni Mubarak. Wan nan hukunci ta baiwa tsohon PM Ahmed Shafiq wadda yayi aiki da Hosni Mubarak, damar shiga zaben fidda gwanin.Shafiq ne yazo na biyu a zaben farko wadda wani dan kungiyar Muslim Bortherhood yazo na daya.

Haka kuma kotun ta yanke hukuncn cewa sulusin wakilan majalisar dokokin kasar an zabe su ba bisa ka’ida, sabo da haka gaba majalisar baki dayan ta ta saba doka, domin haka sai a rusa ta.

Samun labarin hukuncin ya fusata mutane masu yawa, wadanda suka hallara a harabar kotun suka fara kiraye kirayen kifar da gwamnatin mulkin sojan kasar.

XS
SM
MD
LG