Kamar yadda a ka sanar tun farko, tawagar alhazan Najeriya ta karshe ta sauka a Jeddah bayan tashi daga filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Rukunin na karshe na cikin adadin alhazan jihohi dubu 44,450 banda maniyyatan dake tafiya ta jirgin yawo.
Hukumar alhazan ta bayyana cewa a dauki matakan ganin cewa mahajjata sun sami kular da ya kamata ta wajen ajiye jami’in hukuma a dukan wuraren da aka sauke mahajjata. Aka kuma kara jan hankalin masu aikin hajin su kula bayan samun labarin wadansu suna kokarin damfarar alhazan da suka fahimci cewa, suna bukatar taimako. Ta dalilin haka suka takaita shigowar baki masaukan alhazai a Makkah da Madina don lamuran tsaro.
Saurari cikakken rahoton Saleh Shehu Ashaka
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.