Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanonin Sadarwa Na 'Ci Gaba Da Zaluntar Najeriya Kan Kudin Haraji.


Daya cikin kamfanonin sadarwar Najeriya
Daya cikin kamfanonin sadarwar Najeriya

Akwai 'yan Najeriya kimanin miliyan 150 dake anfani da wayar salula,Muryar Amurka ta gano wasu suna cutar gwamnati Nera 20 akan kowane kira daga kasar waje, lamarin da hukumar NCC ta ce zata shiga kafar wondo daya da mazambatar.

Hukumar dake kula da harkokin kanfunan sadarwa a Najeriya, ko NCC atakaice, ta fitar da alkaluman dake nuna cewa kawo yanzu akwai 'yan Najeriyan kimanin miliyan 150 da suke anfani da wayar salula a cikin kasar.

Hanyar sadarwar tana taimakawa tattalin arzikin kasa domin kuwa kowane kwata ko watanni uku tana samar ma kasa kudin shiga da suka kai Nera miliyan dubu daya.

Sai wani bincike da Muryar Amurka ta yi, ya nuna cewa wasu bata gari na cutar gwamnati ta boye sarsalar inda kira ya fito musamman daga kasashen waje, sai su mayar dashi tamkar na cikin gida su biya gwamnati farashin cikin gida kana su jefa sauran a aljihunsu.

Daya cikin 'yan kwamitin sadarwa na majalisar dattawan Najeriya Sanata Muhammad Ubale Shittu, ya ce majalisar zata dauki kwakwaran matakai saboda suna sane da matsalar.

Shi ko shugaban hukumar dake kula da kamfanonin sadarwa ko NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta ya ce tuni hukumar ta fara daukan matakan jan kunne da tsawatarwa tare da zuwa kotu idan ta kama su yi hakan. Mataki na karshe shi ne dakatar da lasisin su.

Wasu 'yan Najeriya na cewa wayar sadarwa ta zama masu jiki ko rayuwa saboda haka ba zasu kushe mata ba.

Ga karin bayani daga rahoton Medina Dauda

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:59 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG