Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Na Tsokaci Akan Cutar da Kamfanonin Sadarwa Ke Yiwa Kasar


MTN, daya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa na Najeriya
MTN, daya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa na Najeriya

Yayin da masu amfani da wayoyin sadarwa a Najeriya ke ci gaba da kokawa dangane da yadda kamfanonin sadarwa ke cutar dasu, masu sharhi kan al’amura da kungiyoyin sa kai sun bukaci hukumar kula da kamfanonin sadarwar ta gaggauta daukar mataki ko kuma shugabannin ta su sauka daga mukaman su.

Aika da sakonnin da ba ka nema ta wayar salula ba a kuma cire kudinka ko kuma a kira mutuum daga kasashen ketare lambar daya daga cikin kamfanonin gida ta bayyana a wayarsa, abu ne da ya zama ruwan dare a tsakanin ma’abuta amfani da wayar salula a Najeriya.

Wani ya ce yana da dan'uwa dake karatu a kasar waje amma da ya kira sai ya ga lambar cikin gida ta bayyana. Da ya tambayeshi sai yace jama'a da dama da yake kira lambar Najeriya ce take bayyana. Haka ma idan ya sa kudi a wayarsa kafin ya ankara kudin ya kare. Daga karshe ma sai ya daina amfani da wayar MTN

Malam Abdulganiyu Rufa’i, kwararre ne kuma Masani kan harkokin fasahar sadarwa ta zamani ya yi tsokaci game da wannan batu. Ya ce kananan kamfanoni bai zama dole suna harkar sadarwa ba. Su ne suke sayen ijina suna hada baki da manyan kamfanoni suna karbar kira daga kasashen waje su dora kan lambar gida kiran ya tafi inda ya nufa. Wannan harkar sana'a ce. Idan kasa ta amince da hakan babu komi idan kuma bata sane da hakan to akwai matsala. Hukuma ce take da hurumin daukan matakan da suka dace.

A makon jiya dai kamfanin MTN, guda cikin kamfanonin sadarwa a Najeriya, ya fadawa Muryar Amurka cewa, wasu bata garin kamfanoni ne ke haddasa matsalar.

Kodayake shugaban hukumar kula da kamfanonin sadarwa a Najeriya Farfesa Garba Umar Danbatta yace suna bincike tare da daukar matakin shari’a game da batun, amma ga alama ‘yan Najeriya irin su Comrade Yahya Shu’aibu Ungogo ba su gamsu ba.

A cewar Ungogo magana ce ta tsaron kasa kuma ta tattalin arzikin kasa. Tunda shugaban hukumar NCC ya fada suna sane kuma bai yi komi ba ya kamata ya sauka daga mukaminsa inji Ungogo. Lamarin ya nuna ana sakaci kuma kamata yayi a yi bincike mai zurfi injishi.

Ga alama dai, matsayar Yahya Shu’aibu Ungogo na alkibila guda data daraktan cibiyar CAJA mai rajin fadakar da Jama’a da wanzar da shugabanci na gari, comrade Kabiru Sa’idu Dakata.

Datkata ya ce "Abun takaici shi ne su hukumomin dake kula da wannan alhaki musamman hukumar NCC...ikirarin cewa tana tarawa gwamnati makudan kudi tatsar talakawa ake yi kuma su hukumomin sun sani cin amanar talakawa ne kuma suna ganin ya cancanta shugabannin hukumomin ko su sauka ko kuma su fito su nemi gafara daga 'yan Najeriya tare da takura kamfanonin sadarwa su biya 'yan Najeriya wata diyya da kuma alkawarin a daina wannan shakiyancin".

Bayan NCC Kwamred Sa'idu Dakata ya kira sunayen wasu hukumomin dake da alaka da harkokin sadarwa su fito su yi bayani.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG