Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya Milyan 2.3 Sun Yi Rijistar Rigakafin Cutar Korona Kasa Da Sa’o’i 24.


A health worker holds up a vial of Covishield, AstraZeneca-Oxford's Covid-19 coronavirus vaccine, at the Ayeyarwady Covid Center in Yangon on January 27, 2021. (Photo by Sai Aung Main / AFP)
A health worker holds up a vial of Covishield, AstraZeneca-Oxford's Covid-19 coronavirus vaccine, at the Ayeyarwady Covid Center in Yangon on January 27, 2021. (Photo by Sai Aung Main / AFP)

Hukumar lafiya matakin farko ta Najeriya wato NPHCDA, ta kawar da fargabar yiyuwar ‘yan kasar ba za su so a yi musu allurar rigakafin cutar Korona birus ba.

Hukumar ta NPHCDA ta bayyana cewa, a cikin kasa da sa’o’i 24 da karbar rigakafin, ‘yan Najeriya kimanin milyan 2 da dubu 300 sun yi rijistar nuna sha’awar karbar rigakafin.

Duk da dai akwai fargaba kan amincin rigakafin na korona, babban daraktan hukumar lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib, ya ce akwai annashuwa a Najeriya game da isowar rigakafin cutar ta korona nau’in AstraZeneca milyan hudu a ranar litinin cikin kasar.

Jamian Najeriya sun karbi rukunin farko na rigakafin corona a Abuja
Jamian Najeriya sun karbi rukunin farko na rigakafin corona a Abuja

Duk da haka Dakta Faisal ya bayyana cewa, akwai jan aiki a gaban gwamnati, kodayake isowar rigakafin rukuni na farko zai karfafawa Najeriyar gwiwa a yaki da take yi da cutar korona da ‘yan kasar sama da dubu 150 suka kamu da ita.

Ya kara da cewa wannan ne ya sa hukumarsa ta dauki aikin yaki da cutar da mahimmanci kuma za a kara himma wajen aikin da ke gaban su domin cimma nasara.

"Hakika rigakafin sun iso Najeriya, sai dai akwai aiki ja a gaba na tabbatar da cewa an baiwa ‘yan kasar ta yadda ya kamata ba tare da matsala ba" in ji Dr. Faisal.

Ya ce hukumar lafiya a mataki na farko ta yi tsari a kan yadda za a bada allurar rigakafin kuma a halin yanzu, tana jiran amincewa daga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa wato NAFDAC sannan ta fara bayarwa.

Jamian Najeriya sun karbi rukunin farko na rigakafin corona a Abuja
Jamian Najeriya sun karbi rukunin farko na rigakafin corona a Abuja

Babban daraktan hukumar ta NPHCDA, ya kuma bukacin ‘yan Najeriya su yi watsi da jita-jitar cewa, jiga-jigai da masu ruwa da tsaki da sauran manya a kasar ne kadai za'a baiwa rigakafin.

Ya tabbatar da cewa, za'a baiwa ma’aikatan kiwon lafiya da ke kan igaba a yaki da cutar da mutanen da ke fama da cutar, sannan a baiwa sauran yan Najeriya.

A nasa bangare, mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya jadadda cewa, za'a yi amfani ne da tsarin baiwa ma’aikatan kiwon lafiya da suka sadaukar da kan su a wajen aikin kula da marasa lafiya, wanda shugaban kwamitin ko-ta-kwana a yaki da cutar korona birus, Boss Mustapha ya ayyana a lokacin taron manema labarai da suka saba gudanarwa kan rabon rigakafin.

Ban da ma’aikatan kiwon lafiya da ke kan gaba a karbar rigakafin korona, farfesa Yemi Osinbajo, ya ce wasu daga cikin shugabannin kasar zasu biyo baya wanda ya ce hakan zai yi tasirin wajen karafafawa ‘yan kasa gwiwa kan sahihancin rigakafin su ma su karba.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG