Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Nijer Mazauna Najeriya Sun Yi Liyafar Kafa Sabuwar Gwamnati


Yan Nijar
Yan Nijar

Al'umman Nijer mazauna Babban Birnin Tarrayyar Najeriya Abuja sun yi wata kwaryakwaryar liyafa na nuna farin cikin su da yadda aka samu sabuwar gwamnati cikin kwanciyar hankali.

Wanan farin ciki na su ya biyo bayan rantsar da Shugaba Mohammed Bazoum da aka yi a kasar Nijer da shi ne karon farko da shugaban gwamnatin farar hula ya mika wa farar hula mulki, wanda yin haka ya nuna dorewar tafarkin damokradiya.

Yan Nijar
Yan Nijar

Shugaban yan Nijer a Abuja Alhaji Usman Mohammed ya ce suna murna kwarai da gaske tare da fatan shugaban kasa Mahammed Bazoum zai yi kokarin kawo hadin kan yan kasar Nijer sannan ya tabbatar da tsaro da samarwa matasa ayyukan yi. Usman Mohammed ya ce in har an samu wadanan abubuwa uku to Nijer za ta samu cigaba mai dorewa.

A na shi bayanin, daya daga cikin 'ya'yan Jamiyar adawa ta RDR CHANJI, Hassan Kwase ya yi fatar za a sako masu 'ya'yan Jamiyar su da hukuma ta kame tare kuma da fatan za a jawo su kusa don tafiyar da mulkin kasar.

Saurare cikakken rahoton Madina Dauda cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

XS
SM
MD
LG