Accessibility links

An bayyana 'yan Nijeriya da cewa masu karyar imani ne amma sai aikata masha'ar da ta hana kasar cigaba.

Gwamnan jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi y ace miyagun dabi’u ne ke kawo cibaya a Nijeriya. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin taron Majami’ar Christ Life Church na shekara-shekara.

Ya ce ‘yan Nijeriya sun fi ‘yan Amurka da Rasha da sauran wasu kasashe da dama bautar Allah; to amma halayyansu na yin hannun riga da da ikirarinsu. Ya ce idan da ‘yan Nijeriya za su canza hali da za a sami gagarimin ci gaba a Nijeriya Gwamnan ya kuma roki shugabannin addinai da su taimaka ma gwamnati da addu’o’i.

A na shi jawabin, shugaban Majami’ar Pastor Enoch Adeboye ya bukaci Kirista su kara azama wajen aikata abubuwan kirki da kuma addu’o’I domin a sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.

XS
SM
MD
LG