Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Republican 2 Suka Rage A Majalisa Daga 10 Da Suka Kada Kuri'ar Tsige Trump


Donald Trump
Donald Trump

Mako guda kafin wa’adin tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya kare a watan Janairun bara, ‘yan jam’iyyar Republican 10 a majalisar wakilai sun bi sahun gaba daya ‘yan Democrat wajen kada kuri’ar tsige shi saboda tada tarzoma da aka yi a ranar 6 ga watan Janairu a ginin majalisar dokokin Amurka.

Fiye da shekara guda da rabi bayan haka, sannan kuma bayan kakkausar suka da aka yi ta yi wa ‘yan jam’iyyar Republican da suka fita karara suka yi adawa da shi, Trump ya dauki wani mataki na ramuwar gayya.

Hudu daga cikin ‘yan majalisar 10 da suka kada kuri’ar tsigewar sun zabi yin ritaya idan sun kammala wa’adinsu a watan Janairu mai zuwa, maimakon fuskantar ‘yan takarar da Trump ke marawa baya a zabukan fidda gwani na jam’iyyar.

Bugu da kari, wasu hudu sun sha kaye a rikicin cikin gida da Trump ya goyi bayan wadanda suke kalubalantarsu a cikin ‘yan watannin nan, don haka su ma za su bar majalisar.

Biyu ne daga cikin 10 kawai suka rage masu neman wani wa’adin shekaru biyu da za su shiga zaben watan Nuwamba, inda za su fafata da masu kalubalantarsu na Democrat.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG