Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sa Kai 120 Za Su Yi Zaman Kaso a Madadin Omar Farouq Idan Ta Kama


Piotr Cywinski, Darektan gidan tarihi na Auschwitz-Birkenau
Piotr Cywinski, Darektan gidan tarihi na Auschwitz-Birkenau

Wani fitaccen masanin tarihi na kasar Poland ya rubutawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wasika yana roko a yi wa yaron da kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yankewa hukumcin daurin shekaru 10 bisa laifin batanci ahuwa.

Darektan dakin tarihi na Auschwitz-Birkenau Piotr Cywiński, ya bayyana cewa a shirye ya ke ya yi zaman kaso a madadin Omar Farouq idan ta kama, ya kuma yi alkawarin daukar nauyin ilimantar da yaron domin bashi damar zama dan kasa na gari da kuma bada gudummuwa ga kasarshi a maimakon katse mashi hanzari da tauye rayuwarshi.

A cikin wasikar da masanin tarihi Cywiński ya rubutawa shugaba Buhari, yace idan ba shi yiwuwa a janye wannan hukumcin da aka yankewa yaron, yana kira ga ‘yan sa kai 120 a fadin duniya su daukewa yaron hukumcin, inda kowannensu zai yi zaman gidan yari na wata guda domin cika wa’adin hukumcin da aka yankewa yaron.

Masanin tarihin yace " a matsayina na darektan dakin tarihi na Auschwitz, da yake adanawa da kuma tunawa da wadanda aka kuntatawa da cin mutuncinsu a sansanin Nazi inda kasar Jamus ta kulle kananan yara ta kuma kashe su, ba zan iya rufe baki in kawar da kai ba kan wannan hukumcin da ya zama abin kunya ga bil’adama.”

Ya kara da cewa, "ko da menene ya fada, bai kamata a dauke shi a matsayin wanda ya mallaki hankalinshi ba, sabili da shekarunsa. Bai kamata a tauye mashi kuruciyarshi a kuma hana shi damar ci gaba, a jefa shi cikin halin kunci iya rayuwarshi."

A farkon wannan watan asusun tallafawa kananan yara UNICEF ya kushewa wannan hukumcin da aka yankewa Farouq

Kotun shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta yankewa Omar Farouq hukumcin daurin shekaru goma a gidan yari ne bayan ta same shi da laifin batanci lokacin da wani sabani ya shiga tsakaninshi da wani abokinshi.

Ranar 10 ga watan Agusta, kotun shari’ar Musuluncin ta jihar Kano ta kuma yankewa Yahaya Sharif-Aminu hukumcin kisa sabili da samunshi da laifin batanci. Sai dai kawo yanzu ba a aiwatar da hukumcin ba sabili da lauyoyin da ke kare Yahaya Sherif sun daudaka kara, sai dai gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bada tabbacin cewa zai sa hannu a takardar hukumcin da za ta bada izinin aiwarar da hukumcin da zarar an kawo teburinshi.

Kawo yanzu dai shugaba Muhammadu Buhari bai ce komi dangane da wannan batu ba, bai kuma maida martani kan wasikar da masanin tarihin ya rubuta masa ba. Masu kula da lamura sun ce shugaban kasa yana ikon dakatar da aiwatar da hukumcin da yake ci gaba da daukar hankalin kungiyoyin kare hakkin bil’adama da kuma sauran kashen duniya.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG