Accessibility links

Masarautar Akinyele a Jihar Oyo ta Bayarda Sarautu ga 'Yan Arewa da Dama

  • Garba Suleiman

Baale Bayo Akinsola yace nadin sarautun da aka yi ma wasu shugabannin Arewa, yunkuri ne na karfafa zumunci a tsakanin Yarbawa da 'yan asalin Arewa.

A wani yunkurin karfafa zumunci da hadin kai a tsakanin Yarbawa da 'yan Arewa mazauna yankinta, masarautar Akinyele a jihar Oyo dake yankin kudu maso yammacin Najeriya ta bayarda sarautun gargajiya ga shugabannin al'ummar Arewa dake zaune a cikin masarautar.

A lokacin da yake nadin sarautun, Baale na Akinyele, Bayo Akinsola, ya bukaci sabbin masu sarautar da su zamo jakadu na wanzar da zaman lafiya a tsakanin al'ummominsu da mutanen kasar Akinyele.

Sarautar da aka ba shugabannin na al'ummar Arewa ita ce Baba Duroro na kasar Akinyele da Kewaye. Duk wanda aka nada sarautar, an sanya masa ganye a gefen goshi, alamar mallakar wannan sarauta.

Shugaban al'ummar Hausawa, Alhaji Yaro, daya daga cikin wadanda aka nada bisa wannan mukami, ya bayyana godiya ga Baale na Akinyele da Olubadan na Ibadan da kuma gwamnan Jihar Oyo saboda iznin da suka bayar na wannan nadin sarauta, ya kuma ce wannan dama ce suka samu ta kara karfafa danon zumunci da zaman lafiya a tsakanin 'yan asalin kasar da su da suka maida ta gida a yanzu.

Shi ma shugaban hadaddiyar kungiyar 'yan arewa a Akinyele, Alhaji Audu Ali Bukar, ya bayyana godiya ga shugabannin Akinyele da kuma Sarkin Sasa a saboda wannan sarauta da ya bayyana a zaman matakin karamta Hausawa.

Mai martaba Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin Katsina, Sardaunan Yamma, kuma shugaban majalisar sarakunan Arewa a kudancin Najeriya, yace an ba su sarautar ce a saboda kyawawan halaye da kwazonsu, ya kuma roke su da su ci gaba da nuna wannan domin samun zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG