Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda A New York Sun Kama Shugaban Asusun lamunin Kudi Na Duniya, IMF


Shugaban Asusun IMF, Dominique Strauss-Kahn
Shugaban Asusun IMF, Dominique Strauss-Kahn

An kama Dominique Strauss-Kahn bisa zargin cewa ya nemi tilasta ma wata ma'aikaciyar hotel yin lalata da shi asabar a New York

‘Yan sanda a birnin New York a nan Amurka, sun kama shugaban Asusun Lamunin Kudi na Duniya, IMF, bisa zargin cewa ya nemi yin lalatar karfi da yaji da mai sharar daki a wani hotel na birnin.

Kakakin ‘yan sandan New York, Paul Browne, yace sun kama Dominique Strauss-Kahn kuma su na yi masa tambayoyi cikin daren nan na asabar. ‘Yan sanda suka ce sun fito da shugaban asusun lamunin kudin na duniya dan asalin kasar Faransa daga cikin jirgi da maraicen asabar, ‘yan mintoci kadan kafin wannan jirgi ya tashi zuwa Paris.

Har ya zuwa yanzu ba a rubuta takardar tuhumarsa da wani laifi gaban kotu ba.

‘Yan sanda suka ce wata mai sharar daki a Sofitel Hotel ‘yar shekara 32 da haihuwa, ta ce ta shiga dakin da Strauss-Kahn yake da misalin tsakar rana domin ta share. Matar ta fadawa ‘yan sanda cewa Strauss-Kahn ya fito tsirara daga bayan daki, ya kuma yi kokarin tilasta mata ta yi lalata da shi. Ta samu ta tsere daga dakin ta fadawa sauran ma’aikatan hotel din wadanda suka kira ‘yan sanda.

‘Yan sanda suka ce a lokacin da suka isa hotel din, Strauss-Kahn ya riga ya kama hanyar tafiya filin jirgin sama, inda ya bar wayar salularsa da wasu kayansa a cikin dakin. An ce an yi wa matar jinyar rauni maras tsanani a wani asibiti.

Wani kakakin asusun IMF a nan Washington ya ki yin sharhi kan wannan al’amari.

Strauss-Kahn ya zamo shugaban Asusun Lamunin Kudi na Duniya, IMF a watan Nuwambar 2007. Shi ne tsohon ministan kudi na kasar Faransa, kuma ana daukarsa a zaman babban wanda zai kalubalanci shugaba Nicolas Sarkozy a zaben shugaban kasa na Faransa da za a yi a shekara mai zuwa a matsayin dan takarar jam’iyyar gurguzu ta Socialist.

Wasu ma su na fadin cewa shugaba Sarkozy ya goyi bayan Strauss-Kahn ya zamo babban darektan asusun IMF ne a wata dabarar kawar da shi daga cikin harkokin siyasar Faransa. Strauss-Kahn yana auren wata sananniyar ‘yar jarida mai aikin telebijin a faransa, kuma a can baya ma ya sha fuskantar abubuwan fallasa na yin fasikanci. A shekarar 2008 ya nemi gafara saboda abinda shi da kansa ya kira kuskuren tunani a bayan da yayi lalata da wata ma’aikaciyar asusun na IMF.

XS
SM
MD
LG