Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan sanda a jihar Ondo sun kama daya daga cikin shugabanin kungiyar 'yan Boko Haram


Sojan Nigeria
Sojan Nigeria

'Yan sandan jihar Ondo sun kama daya daga cikin shugabanin kungiyar 'yan Boko Haram mai suna Idris Ibrahim Babawo

Rundunar sojan Nigeria tace ta damke daya daga cikin shugabanin kungiyar Boko Haram mai suna Idris Ibrahim Babawo.

A ranar Lahadi ‘yan sanda a jihar Ondo suka kama Idris Ibrahim Babawo, kuma suka damka shi hannun rundunar soja ta talatin da biyu jiya litinin. Mai magana da yawun rundunar soja, Brigadiya Janaral Usman Sani Kuka Sheka ya baiyana haka a wata sanarwar daya gabatar.

Sanarwar tace shi Idris Ibrahim Babawo da aka kama shekarunsa na haihuwa arba’in da biyu, sa’anan kuma ana kiran sa Idoko ko kuma Nagada. Yana cikin jerin sunayen yan Boko Haram da ake nema.

Shi dai dan asalin kauyen Chinade ne a karamar hukumar Katagum ta jihar Bauchi arewa maso gabashin Nigeria.

Jihar Ondo inda aka kama Babawo tana kudu maso yammacin Nigeria. Babawo ya arce daga arewa maso gabashin Nigeria a saboda kokarin murkushe yan Boko Haram da rundunar soja ta dufuka yi a yankin.

Janaral Usman Sani Kuka Sheka yace Babawo ya gudu ne a saboda kaucewa a kama shi da kuma yiwuwar hukunta shi.

Sanarwar bata baiyana yadda aka kama Babawo ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG