Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Na Bincike Kan Zargin Yunkurin Sace Mutum Takwas Daga Tashar Kawo A Kaduna


Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai

Tuni dai wannan murya ta kai kunnen mahukunta kuma har ma wasu daga cikinsu sun ziyarci tashar ta Kawo don bibiyar lamarin.

A daidai lokacin da jami'an tsaro da wasu gwamnatoci ke nuna damuwa game da masu baiwa 'yan-bindiga bayanan sirri, muryar wata mata da ta karade shafukan sada zumunta inda ta zargi wani direba a tashar Kawo da hada baki don mika ta da 'yan uwanta bakwai ga masu sace mutane ya sa hukumomi sun kaddamar da bincike

Ko da yake, shugabanni direbobi a tashar ta Kawo sun musanta wannan mata inda har suka nemi da ta je ta ba da sheda.

Jahar Kaduna dai na cikin jihohin Najeriya da ke fama da hare-haren 'yan bindiga da kuma sace mutane wanda wannan ne ya sa muryar matar da aka fara yawo da ita a kafafen sada zumunta na zamani a farkon makon nan, ta ja hankalin mutane da dama.

Matar wadda ba ta bayyana sunan ta ba, ta ce da kyar su ka tsira.

Tuni dai wannan murya ta kai kunnen mahukunta kuma har ma wasu daga cikinsu sun ziyarci tashar ta Kawo don bibiyar batun kuma Sakataren kungiyar direbobi ta NURTW, Kwamared Bature Yusuf Suleman ya nuna shakku kana bayanan matar inda ya ce akwai tsarin da suke bi wajen yin lodi a tashar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna CP Mudashiru Abdullahi dai ya ce su na binchike game da wannan zargi.

Da yawan matafiya dai kan shiga tashoshin mota ne don gujewa tarkon mabarnata kuma wannan ne ya sa zargin wannan mata na hadin baki da direban motar da su ka shigo daga tasha ya ja hankalin mutane da dama.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:

‘Yan Sanda Na Bincike Kan Zargin Yunkurin Sace Mutane Takwas Daga Tashar Kawo A Jihar Kaduna - 3'08"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG