Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Na Bukatar Saraki Ya Amsa Zargin Da Ake Masa Cikin Sa'o'i 48


Bukola Saraki
Bukola Saraki

'Yan Sanda sun aikawa Bukola Saraki wasikar cewa ba sai ya kai kansa ofishinsu ba amma ya amsa zargin da ake masa a rubuce cikin sa'o'i 48.

A shafinsa na twitter, Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa, ‘yan sanda sun aiko da wasikar da ta shaida masa cewa ba sai ya kai kansa ofishinsu a, maimakon wannan sun ba shi damar ya amsa zargin da ake masa a rubuce cikin sa’o’i 48 wanda kuma ya ce yana shirin yi.

A ranar Lahadi ne 'yan sanda suka gayyaci shi Saraki zuwa ofishinsu na Guzape da ke Abuja bayan da wasu 'yan fashin da suka tafka fashi da makami a wasu bankunan kasuwanci a garin Offa da ke jihar Kwara suka ce su yaransa ne.

Saraki na ganin wannan wani mataki ne na neman bata masa suna inda ya dangantashi da takun sakar da ke faruwa tsakanin majalisar dattawan da sufeto janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris wanda sau uku ya ki amsa gayyatar da majalisar ta yi masa a kwanakin baya, sai dai ya tura mukaddashinsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG